Daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Afirka MTN Nigeriam, ya tallafawa matasan ‘yan kasuwa a Kano da kudi naira miliyan 5 a matsayin tallafin fara kasuwanci domin taimaka musu wajen kafawa da bunkasa harkokin su.
Tallafin ya kasance wani bangare na shirin “The Gathering on 100”, wani shiri da aka tsara musamman ga matasa wanda ya hada ‘yan kasuwa, masu kirkirar a shafukan sada zumunta, masu kirkire-kirkire da masu tsara al’adu domin sadarwa, kirkira da bayyana kansu.
SolaceBase ta rawaito ce an gudanar da gasar kacici-kacici ta kasuwanci (Pitchathon), tare da baje kolin kirkira, nuna sabbin fasahohin na zamani da wasannin nishadi ciki har da wasan dara, Scrabble da kwallon tebur.
Da yake zantawa da manema labarai, Babban Manajan Tallace-tallace na MTN na shiyyar Arewa maso Gabas, Abu-Sufyan Aliyu, ya ce an tsara shirin ne domin baiwa matasa dama su hadu, musayar ra’ayi, gano basirarsu da habaka sabbin hanyoyin magance matsalolin da za su iya canza al’umma.
A cewarsa, shirin ya nuna jajircewar MTN wajen tallafawa ci gaban matasa ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gano kwarewarsu da cimma burikansu.
“The Gathering on 100” dandali ne da ke hada matasa domin su hadu, su musayar ra’ayi da kuma samar da sabbin hanyoyin magance kalubalen da suke fuskanta. Haka kuma dama ce a gare su ta bayyana kansu su gano kwarewarsu,” in ji shi.
Wacce ta lashe gasar, Samiat Damilola Yusuf, wacce daya ce daga cikin wadanda suka kafa manhajar Applicant, ta nuna godiyarta ga kamfanin MTN saboda karrama kirkire-kirkiren da rukuninsu ya yi.
Ta bayyana cewa Applicant, dandali ne da aka samar da bai wuce watanni 3 da suka wuce, na samar da kudaden shiga ta hanyar taimaka wa kungiyoyi wajen gudanar da shirye-shirye yadda ya kamata.














































