An ji karar harbe-harbe a filin jirgin saman babban birnin Nijar Niamey

1781767999 750x430

An ji karar harbe-harbe a filin jirgin saman babban birnin Jamhuriyar Nijar, Niamey a safiyar Alhamis wanda ya kwashe akalla sa’a daya a na ji, kamar yadda shaidu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safe agogon kasar. (0500 GMT).

Wani jami’in tsaro da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce lamarin ya nuna cewa an kai hari filin jirgin.

Mai magana da yawun gwamnatin Nijar bai ce komai ba dangani da faruwar al’amarin har yanzu.

Nijar, kamar Mali da Burkina Faso, na fama da hare-haren ‘yan ta’adda daga kungiyoyin IS da Al-Qaeda da ke addabar yankin Sahel.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here