Atiku ya gana da Hayatu-Deen bayan matsalar zaben fidda gwani na ADC

1780249991148

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shiga ganawar sirri da abokin hamayyarsa, Hayatu-Deen, a gidansa da ke Legas a matsayin yunƙurin sulhu bayan zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar.

Channels Television ta rawaito a ranar Lahadi, ganawar ta zo ne bayan da Atiku ya zama dan dan takarar shugaban kasa na ADC kuma aka mika masa tutar jam’iyyar bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani.

Lamarin ya biyo bayan rashin amincewar wasu ‘yan takarar kan yadda aka gudanar da zaben.

Zaben da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da Hayatu-Deen suka yi watsi da sakamakon, inda suka zargi an yi sauya-sauya a tsarin jefa kuri’a. Hayatu-Deen ma ya ce ba zai halarci sanar da sakamakon ba.

Bayan nasararsa, Atiku ya roki ‘yan takara da mambobin jam’iyyar da ke da damuwa su manta da ita su hada kai don jam’iyyar gabanin babban zabe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi kira kai tsaye ga abokan takararsa, inda ya ce su hada kai da shi wajen yunkurin da ya bayyana a matsayin yaki don magance matsalolin kasar.

“Musamman, ina gayyatar Rotimi Amaechi da Alhaji Muhammad Hayatu-Deen su hada kai da ni a wannan yakin na ceto dimokuradiyarmu da kasarmu,” ya ce.

Atiku ya jaddada cewa sakamakon zaben fidda gwani bai kamata ya raba jam’iyyar ba, yana mai cewa gasa ta cikin gida bai kamata ta haifar da rarrabuwa kai ba.

“Kamar yadda na fada a baya, babu masu nasara kuma babu masu rashin nasara. Al’ummarmu na kallonmu don jagoranci, kuma na shirya na jagorance su,” in ji shi.

Ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da sauran ‘yan takara da masu ruwa da tsaki domin karfafa jam’iyyar gabanin babban zabe, yana mai cewa, “Zan yi aiki tare da ku duka don ci gaba da gina jam’iyyarmu. Zan yi yakin neman zabe tare da ku kuma idan shugabannin Nijeriya sun bukata, zan yi mulki tare da ku domin gina kasa da za ta yi wa kowa aiki.”

Ganawa da Hayatu-Deen ta zo ne kwanaki kadan bayan Atiku ya ziyarci tsohon gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi a gidansa da ke Abuja, a wani mataki da ake kallo a matsayin wani bangare na yunkurin hada ‘yan jam’iyyar bayan zaben fidda gwani na shugaban jasa da karfafa goyon baya gabanin zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here