Tsohuwar Jarumar Kannywood, Wasila Isma’il ta rasu

1779642553129 496x430 (1)

Tsohuwar Jarumar Kannywood, Wasila Isma’il, ta rasu tana da shekara 46 bayan doguwar jinya.

Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha ne ya sanar da rasuwar tsohowar jarumar a ranar Lahidi a shafinsa na sada zumunta.

Wasu majiyoyi na kusa da marigayiyar, ta rasu da safe ranar Lahadi a Jihar Kaduna bayan fama da doguwar jinya.

Wasila Isma’il ta bar ‘ya’ya hudu, mata uku sai namiji daya.

Marigayiyar na cikin tsofaffin fitattun jarumai na da a masana’antar fim ta Hausa, ta samu shahara sosai bayan ta fito a fim mai suna ‘Wasila’, wanda ta zama abar fada a kowane gida tun sama da shekara goma da suka gabata.

Ta shiga harkar fim a shekarar 1998 kuma ta kasance daya daga cikin mutanen da ake mutuntawa a masana’antar Kannywood.

Baya ga yin fim, marigayiyar ta kuma yi aiki da Liberty Radio da ke Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here