Hukumar Korafe- Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano(PCACC) ta ce ta gayyaci tsohon Shugaban Ma’aikata na jihar, Abdullahi Musa, kan zargin cire kudi daga albashin ma’aikata.
Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Talata a Kano.
Yahaya ya ce ana sa ran Musa zai bayyana gaban hukumar a cikin wannan mako domin amsa tambayoyi kan zargin.
Ya kara da cewa hukumar ta fara bincike kan lamarin, wanda ya sa dole ya bayyana.
“Hukumar na binciken bayanan sirri da suka shafi tsohon shugaban ma’aikata kan cire kudin ma’aikata.
“Hukumar ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi kan zargin. Zai bayyana gaban hukumar cikin mako guda.
“Har ila yau, mun yi wa gidansa alama dangane da zargin,” in ji shi. (NAN)












































