Sarkin Kano na 16 a Sarautar Fulani, Malam Muhammadu Sunusi na biyu, ya soki yawan ciyo bashin da Gwamnatin Tarayya ke yi duk da cire tallafin man fetir da aka yi.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), Sunusi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka wallafa a shafin News Central TV a ranar Juma’a. inda yace cire tallafin mai da ‘yancin musayar kudi abu ne da ya zama wajibi, amma kin yin la’akari da lokaci tare da rashin alkilta kudi ka iya zagwanye ci gaban da ake tunanin za a samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki.
Sarkin ya kuma ce Najeriya tana karfafa matatun man kasashen ketare, yayin da aka yi watsi da na gida, hakan kuma matsala ce da ke bukatar daukar mataki na gaggawa.
“Na dade ina fadin cewa bada tallafin mai ba abu ne mai dorewa ba, ba zamu ci gaba da bunkasa matatun man kasashen ketare ba, domin Najeriya kasa ce dake da man fetir.” Inji sarkin.












































