Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, a matsayin muƙaddashin Kwamishinan Ma’aikatar albarkatun Rlruwa ta jihar, ƙarin nauyin da ke nuna amincewar da gwamnati ke da ita a kansa.
Dakta Hashim ya bayyana hakan ne a ranar Litinin ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, inda ya tabbatar da cewa an ɗora masa alhakin kula da harkokin ma’aikatar albarkatun ruwa tare da ci gaba da rike mukaminsa na baya.
Ya ce, wannan ƙarin aiki wata dama ce ta bauta wa al’umma, ya na mai jaddada cewa zai yi aiki tuƙuru domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar Kano, duk da kalubalen da ake fuskanta a ɓangaren samar da ruwa.
A cewarsa, za a ɗauki matakan da suka kamata cikin tsari domin tabbatar da samun sauyi mai ɗorewa.
Haka kuma, ya roƙi Allah da ya ba shi ikon sauke wannan nauyi yadda ya kamata.













































