Gwamnatin tarayya ta fara yunkurin samun sabon tallafin kudi daga kasashen waje da ya kai Dala Biliyan 6, domin tallafawa aiwatar da kasafin kudi da kuma inganta muhimman ayyukan more rayuwa a kasar nan.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana a cikin wasiku daban-daban da ya aikawa majalisar dattawa cewa ana shirin karbo Dala Biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi, sai kuma Dala Biliyan 1 daga Birtaniya.
Kudin Dala Biliyan 5 za a yi amfani da shi wajen cike gibin da ke cikin kasafin kudin shekarar 2026, yayin da Dala Biliyan 1 za a karkata shi ne domin gyaran tashoshin jiragen ruwa na Legas, wanda ke da matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci da sufuri na Najeriya.
Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya gabatar da wannan bukata a gaban sanatoci a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata.
Wannan shirin karbo bashin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin karfafa tattalin arziki da kuma magance matsalolin karancin ababen more rayuwa, musamman a bangaren harkokin jiragen ruwa.
Ana ci gaba da sa ido kan yadda majalisar dattawa za ta dauki wannan bukata, yayin da ake jiran karin bayani kan matakan da za a dauka a gaba.












































