Eid-el-Fitr: Tinubu ya yi kira da a rungumi haɗin kai, zaman lafiya da darussan Ramadan masu ɗorewa

Tinubu Prayer

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da rungumar haɗin kai, zaman lafiya da kuma darussan Ramadan masu ɗorewa yayin da al’ummar Musulmi a fadin ƙasar ke gudanar da bukukuwan Eid-el-Fitr tare da addu’o’i da nazari.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a bayan ya halarci sallar Idi a filin sallar Dodan Barracks, inda ya haɗu da sauran masu ibada wajen kammala azumin watan Ramadan.

Tinubu ya nuna godiya ga Allah bisa jagorantar Musulmi cikin watan Ramadan, yana mai cewa watan mai tsarki ya koyar da darussa masu ɗorewa na sadaukarwa, tausayi, ladabi da kuma ƙaunar bil’adama ga masu ibada.

Ya bayyana cewa darussan Ramadan bai kamata su tsaya a lokacin azumi kaɗai ba, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da nuna alheri, kyawawan ɗabi’u da kuma tallafawa marasa galihu a cikin al’umma har bayan watan.

Shugaban ya kuma yi kira da a ci gaba da yin addu’o’i domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa, yana cewa tsaro alhakin kowa ne wanda ke buƙatar haɗin kai, lura da kuma jajircewa daga dukkan ‘yan ƙasa.

Ya ƙara da cewa wajibi ne ‘yan ƙasa su rika bai wa hukumomin tsaro bayanai masu inganci musamman kan duk wani motsi mai tayar da hankali, tare da mutunta doka a kowane lokaci a fadin ƙasar.

Haka kuma, ya bayyana cewa ziyararsa zuwa ƙasar Birtaniya ta nuna muhimmancin haɗin kai, girmama juna da kuma juriya tsakanin addinai daban-daban, yana mai jaddada buƙatar ci gaba da inganta zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma domin bunƙasa ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here