Babbar kotu da ke zamanta a Ado Ekiti a jihar Ekiti ta yanke wa wani mai suna Olatide Temitope Emmanuel hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Wanda aka yanke wa hukuncin mai shekaru 48 ya kashe wata mata mai suna Falade Bosede, sannan a ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2019 a titin Ajebamidele da ke Otun Ekiti ya yi karyar cewa shi likita ne.
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa laifukan sun saba wa sashe na 316 kuma ana hukunta su a karkashin sashe na 319(1) na dokar laifuffuka, babi na C16 na dokokin jihar Ekiti na shekarar 2012.
Domin tabbatar da karar, mai gabatar da kara Kunle-Shina Adeyemo ya gabatar da shaidu guda Bakwai tare da mikawa kotu bayanan wanda ake kara, rahotannin likitoci da kuma hotunan gawar mamaciyar a matsayin hujjoji.
Wanda ake kara ya kare kansa ta hannun lauyansa Adeyinka Opaleke, amma bai gabatar da wani shaida ba.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Babajide Aladejana ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar ba tare da wata shakka ba cewa sakacin wanda ake kara ne ya janyo mutuwar matar a ranar 24 ga watan Yuni na shekarar 2019.
Mai shari’ar ya ce kotu ta same shi da laifi kamar yadda aka tuhume shi, sannan ya umarci cewa Olatide Temitope Emmanuel a rataye shi har sai ya mutu.













































