Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a Kano ranar Lahadi.
Kiyawa ya ce kamen nada alak da rahotanin da rundunar ta samu cewa yan fashi na amfani da muggan makamai suna kai wa mutane hari akan titunan BUK, Hadejia, Zoo Roads, shatalenan Haj camp da kuma sauaran titunan jihar ta Kano.
Ya kara da cewa kwamshinan yan sadan jihar, Mohammed Usaini ne ya bada umarnin kawo karshin aikin bata gari da ya addabi jihar.
“Mutum 27 da muka kama muna zarginsu su da fashi da makami, sanan mun same su da kayan sata a hannun su.” Inji shi.
Kakakin ya kara da cewa sun same bata garin da wayoyin salola 28, adai-adai-ta sahu 2, batiran waya 18 da kuma wasu muggan makamai.
Ya kuma tabbatar da cewa da zarar sun gama bincike zasu gurfanar da wadanda ake zrgin a gaban alkali.













































