Kotu ta yi watsi da shari’ar Abba Kyari da ‘yan uwansa kan rashin bayyana kadarori

ABBa Kyari court

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta shigar a kan dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari kan zargin rashin bayyana kadarorinsa.

Mai shari’a James Omotosho ya yi watsi da karar da aka shigar a kan Kyari da ‘yan uwansa Mohammed Kyari da Ali Kyari, bayan ya bayyana cewa hukumar NDLEA ta kasa tabbatar da tuhumar da ake musu ba tare da shakka ba.

Mai shari’ar ya ce nauyin tabbatar da laifi ba tare da shakka ba yana kan masu gabatar da kara, wanda a wannan shari’ar suka gaza yi.

Ya kuma bayyana karar da ake yi wa Kyari da ‘yan uwansa a matsayin tsanantawa.

Daga nan kotun ta sallami wadanda ake tuhuma tare da wanke su daga zargin da ake musu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa NDLEA na tuhumar Kyari, tsohon shugaban sashen binciken leken asiri na rundunar ‘yan sanda IRT, tare da ‘yan uwansa biyu kan zargin rashin bayyana kadarori.

Hukumar ta kuma ce ta gano kadarori 14 da suka hada da cibiyoyin kasuwanci, gidajen zama, filayen wasan polo, filaye da gonaki mallakin Kyari, tare da wasu kudade sama da Naira Miliyan 207 da kuma Euro 17,598 a wasu asusun bankinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here