Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamna

images 4 3

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, bayan ta mika masa takardar sanarwa domin ya kare kansa kan zarge-zargen da aka yi masa da suka kunshi laifukan da ka iya jawo tsige shi daga mukaminsa.

A wani zaman majalisar na musamman da aka gudanar a ranar Alhamis, takardar sanarwar da aka karanta a zauren majalisar ta kunshi zarge-zargen rashin da’a mai tsanani a aiki, amfani da mukami ba daidai ba da kuma karya amincewar jama’a.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini, wanda ya yi magana da manema labarai bayan zaman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa shi ne ya gabatar da takardar sanarwar tsige mataimakin gwamnan.

Ya ce mambobi 38 na majalisar dokokin jihar ne suka sanya hannu kan takardar sanarwar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ana sa ran karin bayani kan lamarin nan gaba kadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here