Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar komawa zamanta zuwa 5 ga watan Maris

national assembly

Majalisar Dokoki ta Kasa ta sanar da dage komawa zaman majalisa daga ranar Talata, 24 ga Fabrairu, 2026 zuwa ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026.

Hakan na cikin wata sanarwa da Magatakardar Majalisar Dokoki ta Kasa, Kamoru Ogunlana, ya fitar ranar Litinin.

Ogunlana ya ce an dauki matakin ne domin bai wa kwamitocin majalisar damar kammala zaman kare kasafin kudi da ke gudana a halin yanzu.

Sanarwar ta bayyana cewa yanzu za a koma zaman majalisa a zauren biyu ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026 da karfe 11:00 na safe, tare da bukatar mambobi su lura da sabon jadawalin.

Dage zaman na zuwa ne yayin da majalisar ke nazarin kudirin kasafin kudin shekarar 2026, inda kwamitoci da dama ke ci gaba da tattaunawa da ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi kan kasafinsu.

Ana sa ran Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai za su koma zama da karfe 11:00 na safe a ranar 5 ga Maris domin ci gaba da ayyukan majalisa.

Shugabannin majalisar sun nuna nadamar duk wata matsala da sauyin jadawalin zai iya haifarwa, tare da bukatar mambobi su kiyaye sabon ranar da aka sanya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here