Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 33 bayan harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Gundumar Bui da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Birnin Kebbi.
Usman ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da wasu mahara masu ɗauke da makamai, da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne, suka mamaye yankin da nufin satar shanu.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa ana zargin maharan sun shigo yankin ne ta Ƙaramar Hukumar Gudu ta Jihar Sokoto.
A yayin harin, mazauna Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago sun haɗa kai domin kare kansu.
Mai magana da yawun ’yan sandan ya ce rundunar tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce an tura ƙarin jami’ai da kayan aiki, tare da ci gaba da sintiri domin dawo da zaman lafiya da hana sake faruwar irin wannan hari.
Ya ƙara da cewa rundunar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma al’ummar Ƙaramar Hukumar Arewa baki ɗaya.
Usman ya jaddada cewa hare-haren da suka shafi masu manyan makamai na buƙatar haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Ya buƙaci mazauna yankin da su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ake zargi ta hanyoyin tsaro da aka tanada.
Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su riƙa tunkarar masu makamai kai tsaye saboda haɗarin da hakan ke haifarwa ga rayuka da dukiyoyi.













































