Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ake tsare da shi, zai shafe kwana na biyu a hedikwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC a Abuja.
El-Rufai wanda ya gabatar da kansa domin amsa tambayoyi kan zargin cin hanci a ranar Litinin a hedikwatar EFCC da ke Abuja, jami’an hukumar yaki da rashawa sun tsare shi yayin da suke masa tambayoyi.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa ana yi wa tsohon gwamnan tambayoyi kan zargin Almundahana a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.
Wata majiya daga EFCC ta shaida wa NAN cewa El-Rufai zai kuma kwana a daren Talata tare da masu yi masa tambayoyi na hukumar.
A cewar majiyar, hukumar za ta yi aiki da ƙwazo wajen binciken zarge-zargen da ake yi wa tsohon gwamnan.
Majiyar, wadda ba ta iya tabbatar da lokacin da za a sake shi ko gurfanar da shi a gaban kotu ba, ta ce hakan ya danganta da yadda bincike ke tafiya.
Mai taimaka wa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya kuma tabbatar da lamarin a wata sanarwa, yana mai cewa tsohon gwamnan ya amsa gayyatar hukumar kuma ya tattauna da jami’anta.
A cewarsa, El-Rufai ya yi tattaunawa a sarari kuma mai amfani da masu binciken EFCC.
Ya ƙara da cewa tawagar lauyoyinsa ta bayyana halayyar jami’an a matsayin ta ƙwarewa.
Adekeye ya lura cewa tsohon gwamnan ya ci gaba da kasancewa tare da hukumar bayan tattaunawar da aka yi a ranar Litinin.













































