Gwamnatin Jihar Niger ta yi Allah-wadai da mummunan harin da ya faru a wurin hakar ma’adanai na Zuzungi Kataeregi da ke karamar hukumar Katcha, tare da ba da umarnin rufe wurin na wucin gadi.
Sanarwar da babban Sakatare a Ma’aikatar Ma’adanai, Idris Legbo, ya fitar ranar Juma’a ce ta bayyana hakan.
Ya bayyana lamarin a matsayin na ta’addanci kuma wanda ba za a amince da shi ba, yana mai cewa wani jami’in tsaro ya rasa ransa.
Legbo ya kara da cewa harin ya lalata motar sintiri ta hadin gwiwa tare da zama kai tsaye hari kan halalcin aikin hakar ma’adanai da ikon gwamnati.
Rahotanni na farko sun nuna cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga sabani tsakanin masu safarar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da jami’an tsaro da ke aiki a wurin.
Legbo ya bayyana cewa wurin hakar ma’adanin yana da cikakken lasisi, an amince da shi bisa doka kuma yana bin dukkan ka’idoji da sharuddan da suka dace.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rikicin ya biyo bayan cafke kayan hakar ma’adanai daga masu aiki ba bisa ka’ida ba da jami’an tsaro suka yi a wurin.
Haka kuma rawaito cewa masu safarar sun sayi ma’adanai kai tsaye daga kananan masu hakar ma’adanai, abin da ya hana kamfanin da ke da lasisi cin moriya, sannan suka sake sayarwa ga kamfanonin da ba su da rajista.












































