Yan ta’adda sun kashe sojoji biyar da jami’in ɗan sanda ɗaya bayan kai wa dakarun FANSAN YAMMA na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma kwanton ɓauna a kan hanyar Bingi–Kekun Waje–Gusau a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne yayin da dakarun ke dawowa daga jerin hare-haren farmaki da suka yi cikin nasara a tsakanin Birnin Magaji da Anka, inda suka gudanar da ayyukan tsaro masu ƙarfi a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Rundunar FANSAN YAMMA ta bayyana cewa dakarun sun samu nasarori a baya-bayan nan ta hanyar kai samame, kwanton ɓauna da sintiri na faɗa, inda suka cafke wasu mutane uku tare da kashe wasu ’yan ta’adda, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin dazuka.
Yayin farmakin an gano kayayyakin yaƙi da suka haɗa da bindigar PKT, bindigogi AK-47 guda biyar, alburusai da mujallu, na’urorin sadarwa da kuma babura guda uku.
An kuma bayyana cewa yayin da dakarun ke amsa kiran gaggawa kan harin ramuwar gayya da ’yan ta’adda suka kai, sai aka yi musu kwanton ɓauna a Gidan Wagni a kan hanyarsu ta zuwa Kekun Waje, inda aka gwabza faɗa mai tsanani.
Duk da cewa an yi harin ne ba zato ba tsammani, dakarun sun nuna jarumtaka wajen daƙile ƙarin barazana ga al’ummomin da ke kusa, sai dai a fafatawar ne sojoji biyar da jami’in ɗan sanda ɗaya suka rasa rayukansu.
Bayan harin, an tura ƙarin dakarun kai ɗauki ciki har da rundunar kai martani ta birgedi na ɗaya daga sansanonin Kanoma da Kekun Waje, inda suka tilasta wa ’yan ta’adda ja da baya, tare da jikkata wasu manyan shugabannin ’yan bindiga, yayin da ake ci gaba da bin sawunsu domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.













































