2026: Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Sha’aban na shekarar 1447

d6764bb9 ee43 48f7 9b16 7874af898bf5 e1663538043755

Majalisar masarautar Sarkin Musulmi da ke Sokoto ta umarci musulmi a faɗin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1447 AH a ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026.

Sanarwar ta fito ne daga majalisar shawara kan harkokin addini ƙarƙashin majalisar masarautar Sokoto, wadda wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin, Farfesa Sambo Junaidu, ya sanya wa hannu.

Majalisar ta bayyana cewa ranar Litinin ta yi daidai da ranar 29 ga watan Rajab 1447 AH, wadda a addinin Musulunci ita ce ranar da ake fara duban jinjirin watan Sha’aban domin sanin farkon sabon wata.

An bukaci daukacin al’ummar Musulmi da su shiga aikin duban watan tare da bayar da rahoton duk wani sahihin gani ga hakimin gunduma ko na ƙauye mafi kusa domin isar da shi ga mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, wanda kuma shi ne shugaban majalisar Musulunci ta ƙasa.

Majalisar ta jaddada cewa aikin duban wata nauyi ne na addini da ke bukatar himma da gaskiya daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da bin ka’idojin Musulunci yadda ya dace.

Haka kuma majalisar ta yi addu’ar Allah ya sa a samu nasara a aikin duban watan tare da bai wa al’ummar Musulmi shiriya da dacewa wajen aiwatar da wannan ibada ta addini.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here