Ƴan jarida bakwai sun rasu a hatsarin mota a Gombe

Gombe road accident 720x430

Ƴan jarida bakwai, mafi yawansu daga reshen gidan talabijin na ƙasa na NTA ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa NUJ, sun rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da bas ɗinsu a kan titin Billiri zuwa Gombe yayin da suke dawowa daga ɗaurin aure na wani abokin aikinsu.

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC ta tabbatar da cewa mambobi bakwai na ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa NUJ sun rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka jikkata a hatsarin mota guda ɗaya da ya shafi bas ɗin NUJ a jihar Gombe.

Kwamandan sashen FRSC na jihar Gombe, Samson Kaura, ya bayyana cewa mutane 11 ne gaba ɗaya ke cikin motar a lokacin hatsarin, inda tayar mota ta fashe wanda ya haddasa faduwar bas ɗin.

Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin yayin da ‘yan jaridan ke dawowa daga bikin aure da aka gudanar a yankin sanatan Gombe ta Kudu, inda suka je domin girmama wani abokin aikinsu daga gidan talabijin na ƙasa NTA.

Wani ɗan jarida a Gombe ya bayyana cewa waɗanda suka rasu sun haɗa da manyan jami’ai da ma’aikatan NTA da NUJ, yayin da waɗanda suka tsira ke karɓar kulawar likita sakamakon munanan raunuka da suka samu a hatsarin.

Rahotanni sun nuna cewa halin wasu daga cikin waɗanda suka jikkata na da tsanani, yayin da aka buƙaci addu’o’i domin samun sauƙin murmurewa, tare da yin fatan Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, ya ba iyalansu da abokan aikinsu haƙurin jure wannan babban rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here