Sojojin sashen 8 na rundunar sojan Najeriya sun kashe fitaccen shugaban ’yan fashi Kachalla Kallamu a yankin Sabon Birnin jihar Sokoto, yayin wani babban samame da rundunar ta gudanar tare da taimakon masu sa-ido na yankin.
Wani tushe daga jami’an tsaro ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa Kallamu, wanda ya kasance mafi kusa da jagoran ’yan fashin nan Bello Turji, an kashe shi ne tare da wani babban mai kai masa kayan aiki a safiyar Litinin a kauyen Karawa.
Rahotanni sun nuna cewa Kallamu, dan asalin Garin-Idi a Sabon Birni, ya sha addabar al’ummomin yankin, bayan dawowarsa daga gudun hijirar da ya yi zuwa Kogi sakamakon wani samamen sojoji a watan Yuni 2025 da ya sanya ya tsere daga yankin.
Gwamnatin jihar ta yaba da wannan nasarar, inda mai bada shawa kan harkokin tsaro Ahmad Usman ya bayyana cewa sojoji sun dakile yunkurin ’yan fashi da suka kai wa matafiya daga Tarah zuwa kasuwar mako, tare da kashe da dama daga cikinsu ba tare da asarar jami’in soja ba.
Wasu mazauna Tarah da Karawa sun tabbatar cewa sojoji daga sansanin Kurawa sun yi artabu da ’yan ta’adda na tsawon sa’o’i, inda suka kashe tara daga cikinsu, sannan suka gano gawarwaki hudu a cikin daji, tare da kwato bindigogi da alburusai masu yawa, a wani samame da Operation Fansan Yamma ta aiwatar.
Mazauna Gatawa da kauyuka makwabtansa sun bayyana cewa sojoji tare da masu sa-ido sun dakile wani sabon hari da ’yan fashi suka kai yankin, lamarin da ya sa jama’a suka yi murnar nasarorin da ake samu, tare da rokon ci gaba da ayyukan kawar da ’yan ta’addan domin kare fararen hula.
Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Sabon Birni, Aminu Boza, ya tabbatar da cewa gawarwaki tara da ake zargin ta ’yan ta’adda ce aka gani, yayin da ake ci gaba da bincike, tare da tunawa cewa kauyukan Gatawa da makwabtansa sun sha fama da hare-hare a watannin da suka gabata.











































