Janar Faruk Yahaya ya musanta zargin alaƙa da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, ya yi barazanar ɗaukar matakin doka

Faruk Yahaya 1 457x430 (1)

Tsohon babban Hafsan rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya mai ritaya ya karyata zargin da ake danganta shi da wasu mutane da ake zargi da hannu a daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Zargin ya samo asali ne daga bayanan da Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya ya yi, wanda jaridar Sahara Reporters ta wallafa, yana danganta tsohon hafsan sojin da wasu da ake zargi a cikin harkar.

A wata sanarwa da aka fitar a madadinsa ta hannun Birgediya Janar Sani Usman mai ritaya a ranar Asabar a Abuja, Yahaya ya bayyana zargin a matsayin ƙagaggun kalamai marasa tushe kuma ba gaskiya ba.

Sanarwar ta ce a duk tsawon aikinsa kafin ya hau kujerar babban hafsan soji, a lokacin da yake kan muƙamin, ko bayan saukarsa ba shi da wata alaƙa kai tsaye ko a kaikaice da duk wanda ake zargi da ba da gudunmawar ta’addanci ko aikace-aikacen da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Karanta: Buratai ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan jaridar Internet da wani Janar mai ritaya kan danganta shi da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci

Yahaya ya zargi Ali-Keffi da yin bita da kulli saboda matakan ladabtarwa da aka ɗauka a kansa a lokacin da yake cikin aiki, yana mai cewa wannan rubutu na Sahara Reporters ya ginu ne kan mugunta ba tare da wata hujja ba.

Ya kuma soki jaridar Sahara Reporters saboda wallafa zargin ba tare da tantance gaskiyarsa ba, yana mai cewa hakan rashin ɗabi’a ne da ke rage amincewar jama’a ga rahoton jaridu.

Sanarwar ta jaddada cewa wadannan kalamai ba su dace da tarihin aikin Janar Yahaya na gaskiya ba, ƙwarewa da sadaukarwa wajen kare Najeriya.

Tsohon hafsan sojin ya nemi Ali-Keffi da Sahara Reporters da duk masu yaɗa rahoton su janye shi nan-da-nan, tare da ba da uzuri, in ba haka ba zai ɗauki matakin doka domin kare mutuncinsa.

Ya tabbatar da cewa yana da cikakkiyar niyya ga ci gaba da tallafa wa yaki da ta’addanci a Najeriya, yana mai cewa wannan aiki yana buƙatar gaskiya, kishin kasa da bin ka’ida ba yaɗa bayanan da ke kunshe da son rai ko bita da kulli ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here