Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa tana gudanar da bincike a kan ikirarin cewa an janye dakarun tsaro jim kaɗan kafin ’yan ta’adda su sace dalibai mata na makarantar sakandare da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.
An sace dalibai ashirin da biyar daga makarantar a ranar sha bakwai ga watan Nuwamba, lamarin da ya haɗa da kashe mataimakin shugaban makarantar yayin harin da aka kai yankin.
Daraktan ayyukan yaɗa labarai na rundunar tsaro, Manjo janaral Michael Onoja, ya bayyana cewa an fara tantance bayanan da suka danganci ikirarin gwamnan jihar Kebbi cewa ’yan ta’adda sun kai hari kusan mintuna talatin bayan janyewar jami’an tsaro daga yankin.
Ya ce rundunar tsaro na nazarin bayanan da suka shafi yadda aka tura dakarun a lokacin, tare da tabbatar da cewa duk wani gibin tsaro da aka gano zai jawo ɗaukar matakin gaggawa domin gyara matsalar.
Karin labari: Makarantar Catholic a Neja: Ɗalibai da Makamai 227 aka sace – ƙungiyar kiristocin Najeriya
Onoja ya ce sojoji na bin dukkan bayanan sirri da ke da alaka da lamarin domin tabbatar da ceto daliban da aka sace, tare da haɗa kai da hukumomin jiha da shugabannin al’umma da sauran jami’an tsaro wajen tsaurara kariya a makarantu da yankunan da ke cikin haɗari.
Ya bayyana damuwar hedikwatar tsaro game da sace dalibai a Kebbi da kuma na makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja, inda ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na gudanar da ayyuka cikin haɗin kai domin ceto waɗanda aka sace.
Hedikwatar tsaro ta tabbatar wa jama’a cewa tana bibiyar karuwar matsalolin tsaro a wasu sassan arewacin ƙasar, tare da nanata cewa rundunar sojoji za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
NAN













































