Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin gyaran dokar zabe da aka sake yin aiki a matsayin doka.
An yi bikin rattaba hannun ne a fadar shugaban kasa, ranar Juma’a tare da halartar shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da sauran su.
Solacebase ta ba da ruwaito cewa an sanya hannun a karfe 12.25 na Ranar juma’a.










































