Binciken Tsigewa: Kwamitin ya gabatar da rahoto kan Mataimakin Gwamnan Zamfara

Zamfara
Zamfara

Kwamitin bincike mai mutum bakwai da babbar alkaliyar jihar Zamfara Kulu Aliyu ta kafa domin binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan jihar Mahadi Aliyu Gusau ya mika rahotonsa ga majalisar dokokin jihar.

Shaidu bakwai daga cikin wadanda suka shigar da karar sun ba da shaida a gaban kwamitin a zaman da aka shafe kwanaki biyu ana yi, duk da cewa mataimakin gwamnan bai bayyana a gaban kwamitin binciken ba.

Majalisar dokokin jihar Zamfara na zargin mataimakin gwamnan da yin Gadara ga kundin tsarin mulki, da almubazzaranci da kudade, da rashin da’a da kuma cin zarafin.

Solacebase ta ruwaito cewa Mai shari’a Halidu Tanko-Soba mai ritaya shine shugaban kwamitin, yayin da Oladipo Okpeseyi (SAN), Abdul-Atadoga Ibrahim (SAN), Hussaini Zakariyau, (SAN), Amina Tanimu-Marafa, Alhaji Sani Mande da Ahmad Buhari-Rabah, sune mambobi.

A ranar Litinin, Sakataren Kwamitin, Sani Tsafe, ya tabbatar da cewa ya bi duk hanyoyin da suka dace domin domin sanar da mataimakin Gwamnan kan halin da ake ciki.

Tsafe ya shaida wa kwamitin cewa ya aika da sanarwar zuwa ga amintattun imel da kuma dandalin WhatsApp na Aliyu-Gusau, kuma ya gabatar da kwafin da aka tantance a matsayin shaida na samun nasarar isar.

Da yake mika rahotonsa ga manyan jami’an majalisar dokokin jihar Zamfara, shugaban kwamitin Justice Halidu Tanko Soba, ya ce kwamitin ya yi adalci kan duk wasu zarge-zargen da aka gabatar a gabansa.

Shugaban wanda Oladipo Okpeseyi ya wakilta, ya ce kwafi biyu ne kawai na rahoton kwamitin ya samar da shi.

Ya kuma bukaci majalisar da ta rufa wa wannan rahoto asiri kamar yadda ya kamata.

Da yake mayar da martani, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Nasiru Magarya ya tabbatar wa kwamitin cewa majalisar za ta tabbatar da adalci yayin da take duba rahoton.

Shugaban majalisar ya kara da cewa za a yi amfani da rahoton ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima

Gabatar da rahoton na zuwa ne kasa da sa’o’i ashirin da hudu bayan kwamitin ya kammala zaman sauraron ra’ayoyin jama’a tare da tabbatar da cewa zai yi adalci ga dukkan bangarorin.

A kwanakin baya ne mataimakin gwamnan yayi wani taron manema labarai a Abuja yace bashi da kwarin gwiwa akan kwamitin kuma duk wani yunkuri na tsige shi ya sabawa doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here