Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya ayyana kwanaki bakwai na makoki a ƙasar tare da shirya jana’izar ƙasa domin nuna alhinin mutuwar jagoran adawa, Raila Odinga, wanda ya rasu a ranar Laraba.
Ruto ya bayyana Odinga a matsayin ɗaya daga cikin manyan jaruman dimokuraɗiyya a Afirka, ɗan gwagwarmaya marar jin tsoro kuma wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin ana gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci a Kenya.
Shugaban ƙasar ya ce zai dakatar da dukkan al’amuran sa na jama’a a cikin kwanakin makokin, a matsayin girmamawa ga marigayin.
Odinga, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau biyar, ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara siyasar ƙasarsa tun shekaru aru-aru.
Ya rasu yana da shekara 80 a kasar Indiya, inda yake jinya a birnin Kochi.
Rahotannin kafofin labarai na ƙasar Indiya sun bayyana cewa ya mutu bayan samun bugun zuciya yayin tafiya da safe.
A shekarar 1982, Raila Odinga, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa na farko, Oginga Odinga, an kama shi da laifin cin amanar ƙasa bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi wa tsohon shugaban ƙasa Daniel arap Moi, kuma aka tsare shi tsawon shekaru shida ba tare da shari’a ba.
A lokacin mulkin Moi, Odinga ya sha kamu saboda gwagwarmayarsa ta neman rushe tsarin jam’iyya ɗaya, inda daga ƙarshe ƙoƙarinsa ya taimaka wajen kafa tsarin jam’iyyu masu yawa a 1991, da kuma samar da sabonkundin tsarin mulki a 2010, manyan nasarori da suka kafa tarihi a siyasar Kenya.












































