Malala ta ziyarci Najeriya domin ƙarfafa ilimin ƴaƴa mata

Nobel laureate Malala Yousafzai 687x430

Gwarzuwar Nobel, Malala Yousafzai, ta isa Abuja domin ganawa da hukumar gudanarwa ta gidauniyar Malala da nufin ƙarfafa manufofin da suka shafi ilimin ’yan mata a Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar a Najeriya, Nankwat Dakum, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

A cewar Dakum, Malala za ta halarci taron tare da mahaifinta kuma wanda suka kafa hukumar tare, Ziauddin Yousafzai, da shugabar hukumar, Lena Alfi, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa.

Ta ce abubuwan da suka fi mayar da hankali sun haɗa da ba da dama ga ’yan mata da suka yi aure ko suka samu ciki su koma makaranta, ƙara kuɗaɗen da ake warewa domin ilimin ’yan mata, da kuma amfani da ilimi a matsayin mafita wajen kawo ƙarshen auren yara.

Haka kuma, Malala za ta gana da ’yan mata da kuma masu fafutukar ilimi da hukumar ke tallafawa domin jin labarinsu kai tsaye, da abubuwan da suke son ganin sun canza a cikin al’ummominsu.

Bugu da ƙari, za ta yi muhimman tattaunawa da shugabannin gwamnati da na ƙungiyoyin farar hula domin hanzarta ci gaban ilimin ’yan mata a faɗin Najeriya.

Dakum ta jaddada cewa Najeriya na daga cikin ƙasashe da suka fi muhimmanci a dabarun duniya na gidauniyar Malala Fund na shekarar 2025 zuwa 2030.

Ta ce tun daga 2014, hukumar ta zuba sama da dala miliyan takwas ($8m) a cikin ƙungiyoyin abokan hulɗa na Najeriya domin rushe shingayen da ke hana ’yan mata zuwa makaranta.

Ziyarar Malala ta zo a wani lokaci mai muhimmanci inda gwamnati, ƙungiyoyin farar hula da abokan hulɗa na ƙasashen waje ke ƙoƙarin ƙarfafa alƙawuran da za su bai wa kowace yarinya damar yin karatun shekara 12 cikin aminci da inganci.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa gidauniyar Malala ta riga ta ware dala miliyan 50 ($50m) a duniya domin yaki da matsalolin da ke hana ’yan mata samun ilimi, inda kaso mai yawa daga ciki aka tanada ga Najeriya.

Wannan na cikin sabon tsarin shekaru biyar na hukumar mai taken: “Ƙarfafa haƙƙoƙi da Samun Albarkatu domin Ilimin Sakandare na ’Yan Mata.”

Gidauniyar Malala, wacce aka kafa a shekarar 2013 ta hannun Malala da mahaifinta Ziauddin Yousafzai, na fafutukar tabbatar da kowace yarinya ta samu ilimi kyauta, ingantacce, kuma cikin tsaro har na tsawon shekara 12 a faɗin duniya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here