
Majalisar dokokin Somaliya ta amince da wata babbar yarjejeniyar tsaro da Turkiyya, karkashin yarjejeniyar na shekaru goma.
Turkiyya za ta baiwa sojojin ruwan Somaliya makamai da horas da su tare da tura jiragen ruwanta a cikin ruwan Somaliya.
Manazarta sun ce babban mataki ne na inganta tsaron tekun Somaliya.
Karanta wannan: MDD ta ware dala miliyan 100 don ayyukan jinkai a kasashe 7
Firaminista Hamze Abdi ya ce yarjejeniyar ta kawar a fadarsa tsoron ta’addanci da fashin teku da kamun kifi ba bisa ƙa’ida ba da kuma zubar da gurɓataciyar shara.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da cece-kuce da jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta, wadda ta ƙara fargaba tsakanin Mogadishu da Addis Ababa.
Somaliya, wacce ta ɗauki Somaliland a matsayin wani yanki na kasarta, ta zargi Habasha da take mata hakkinta.









































