Kamfanin jirgin sama na Azman ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sa, ya kuma tura ma’aikata hutun dole

AZMAN New 1
AZMAN New 1

Kamfanin jirgin sama na Azman ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sa, ya kuma tura ma’aikata hutun dole ba tare da biyan su albashi ba.

An tattaro rahoton cewa dakatar da aikin jirgin nada alaka da gama jigilar alhazan Najeriya da akai, inda kamfanin ya tura jirgin wajan gyara domin a duba lafiyar sa.

A wata wasika da jaridar Solacebase ta gani wacce Magaji Mohammed Misau ya sawa hannu ranar 3 ga watan Ogasta ta nuna cewa duk ma’aikatan an tura su hutun dole amma banda ma’aikata ta kwais na kamfanin.
Ma’aikatan da basu a hutun sune Engr. Nuraddeen Aliyu; Engr. Zakaria Al-Najjar; Engr. Peter Abraham; Engr. Aliyu Suleiman Gambo; Engr. Thomas Foloronso; Usman Muhammad Sabo; Sabiu Sabo da kuma Magaji Mohammed Misau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here