Rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an kashe jami’anta uku a wani harin kwanton ɓauna da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Karamar hukumar Bakori ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Aliyu Abubakar, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Laraba a Katsina.
Ya bayyana cewa a ranar Talata, da misalin ƙarfe 12:44 na rana, wasu jami’an ’yan sanda da ke gudanar da sintirin hana aikata laifi na yau da kullum a hanyar Guga zuwa Bakori suka fada kwanton ɓauna da wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne, inda suka rika harbe-harbe ba tare da tsari ba.
Ya ce jami’an sun mayar da martani cikin jarumtaka, inda suka fatattaki harin da aka kai musu.
Sai dai jami’an tsaron uku sun rasa rayukansu a yayin musayar wuta, yayin da wasu jami’ai biyu suka samu raunuka.
DSP Aliyu Abubakar ya kara da cewa an garzaya da jami’an da suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa, kuma a halin yanzu suna karbar kulawar lafiya tare da nuna alamun samun sauki.
Ya kuma bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta fara gudanar da bincike domin gano tare da cafke wadanda suka aikata wannan mummunan hari.
NAN













































