Ƴan sanda sun gano motoci biyu da aka sato daga ƙasar Netherlands aka kawo su Najeriya

WhatsApp Image 2025 10 20 at 18.24.46 1 750x430

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasara wajen yaƙi da laifukan da suka shafi ƙetare iyaka, bayan ta gano da kuma kwato motoci biyu masu tsada da aka sato daga ƙasar Netherlands sannan aka shigar da su cikin ƙasar Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Jami’an sashen haɗin gwiwar ƙasashen duniya na hukumar Interpol dake Abuja, tare da haɗin gwiwar ofishin Interpol na birnin Hague, sun gano motar Toyota C-HR (samfurin 2020) da Toyota RAV4 (samfurin 2019) a wurare daban-daban a jihohin Legas da Akwa Ibom.

Bincike ya gano cewa an sato motar ne daga biranen Amsterdam da Midden-Nederland, sannan aka kai su ta tashar jiragen ruwa ta Antwerp dake ƙasar Belgium zuwa tashar Apapa a Legas, a ƙarshen shekarar 2023.

Bayan gano motocin, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta shigar da ƙara a babbar kotun tarayya dake Abuja domin a karɓe motocin ta fuskar doka.

Bayan kammala shari’a, kotu ta bayar da umarnin a ƙarshe cewa motocin su koma hannun gwamnatin ƙasar Holan ta hannun kamfanin inshorar da ke da su.

Sai dai a ranar 20 ga Oktoba 2025, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta hannun sashen Interpol ta mika motocin da aka kwato ga wakilan kamfanin inshorar da kuma ofishin jakadancin masarautar ƙasar Holan dake Najeriya, wanda hakan ya nuna an kammala aikin dawo da motocin cikin nasara.

Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya yaba da ƙwarin gwiwa da ƙwarewar jami’an Interpol Abuja, tare da jaddada mahimmancin haɗin kai tsakaninsu da abokan hulɗa na ƙasashen duniya musamman ofishin Interpol na Hague.

Ya ce wannan nasara ta nuna kudirin rundunar wajen tabbatar da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro na duniya domin hana masu aikata laifukan satar motoci da safarar su samun riba daga ayyukansu.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta ci gaba da amfani da dabarun leƙen asiri da kuma ƙarfafa haɗin kai da hukumomin ƙasashen waje domin yaƙar dukkan nau’ukan laifuka na ƙetare iyaka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here