Sama da ma’aikatan lafiya ashirin na asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da suka yi mu’amala kai tsaye da mara lafiyar da ya kamu da zazzabin Lassa sun yi gwajin cutar.
Hakazalika, wasu da suka yi mu’amala da marar lafiyar kuma aka gwada su sakamakon binciken ya nuna ba sa dauke da cutar, sai dai mijin matar da sakamakon gwajin sa ya nuna yana dauke da ita.
Shugaban kwamitin ba da shawarar Likitoci na Asibitin, Farfesa Muhammad Abba Suwaid ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar jami’ar yada labarai, Maryam Aminu Usman, a ranar Asabar.
Farfesa Suwaid ya ce an kebe ma’aikatan na wani dan lokaci kuma an tattara jininsu domin gudanar da bincike.
Sai dai sakamakon ya nuna cewa babu daya daga cikinsu da ya kamu da cutar.
SolaceBase ta ruwaito cewa Farfesa Suwaid ya kara bayyana cewa hukumar gudanarwar asibitin ta dauki matakin gaggawa bayan tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa kan wata mata mai dauke da juna biyu ‘yar shekara 22 da aka kawo asibitin a ranar 5 ga Afrilu, 2025.
Ya ce hukumar ta dauki duk matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar a asibitoci da kewaye.
A halin da ake ciki, tun da farko mahukuntan asibitin sun sanar da sashin kula da cututtuka na jihar Kano cewa su bincika domin gano yadda aka yi aka samu marar lafiyar a karamar hukumar Garum Malam, inda aka kawo ta asibitin.
Rahotonni sun ce mijin majinyaciyar, wanda ya kamu da cutar a halin yanzu yana karkashin kulawar sashin kula da cututtuka na jihar Kano.