Zaɓen 2023: Buhari ya umarci jami’an tsaro da su kasance ‘yan ba-ruwanmu

9463b232 fd3b 4d38 a2c1 9dc1e010e6b3
9463b232 fd3b 4d38 a2c1 9dc1e010e6b3

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaron ƙasar da za su yi aiki da hukumar zaɓen ƙasar a lokacin zaɓukan 2023 da ke tafe da su kasance ‘yan ba-ruwanmu, tare da nuna ƙwarewar aiki.

Sannan kuma su nesanta kansu daga duk abubuwan da za su kawo matsala ga ayyukansu.

Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga jami’an ne ranar Laraba a lokacin bikin ƙaddamar da rukunin gidajen jami’an hukumar tattara bayanan sirri a unguwar Idu da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Buhari ya umarci hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun kula da ayyukan rarraba tare da lura da muhimman kayayyakin zaɓe cikin nuna ƙwarewar aiki kamar yadda yake kunshe cikin dokokin hukumomin tsaron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here