Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, da ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Abdulsalam Gwarzo, su tsaya takarar zaɓen 2027.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa amincewar tana ƙarƙashin hukuncin da kotuna za su yanke kan shari’o’in da ke gabansu.
Read also: Mutane sun yi biris da dokar hana fita daga gida a Kano
A gefe guda, hukumar ta ƙi amincewa da ƙorafin ɗan takarar gwamnan jihar Ogun na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu, wanda ya nemi a sake duba matakin cire sunansa daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓe.
Wata majiya a hukumar INEC, wadda ta zanta da jaridar Daily Trust bayan taron hukumar da aka gudanar a ranar Alhamis, ta ce hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa dangane da cire sunayen wasu ’yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi daga jerin sunayen ’yan takara.
Majiyar ta ce an amince da kusan ƙorafe-ƙorafe 36, yayin da aka ƙi amincewa da sauran.
“Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa. An amince da wasu daga cikinsu, ina tsammanin kusan 36, yayin da ba a amince da sauran ba,” in ji majiyar.
Read also: Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka ya fice daga PDP
Sai dai majiyar ta bayyana cewa hukumar na jiran cikakken adadin ƙorafe-ƙorafen da aka amince da su daga sashen shari’arta, wanda ke shirya sanarwar hukuma kan matakan da aka ɗauka.
Dangane da Pantami da Gwarzo, majiyar ta ce hukumar ba ta da wata matsala da tsayawarsu takara, amma ta jaddada cewa shari’o’in da ke gaban kotu na iya shafar cancantarsu.
“Eh, an amince da Pantami,” in ji majiyar lokacin da aka tambaye ta game da ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP.
Game da Gwarzo kuwa, majiyar ta ce amincewar da aka ba shi tana ƙarƙashin hukuncin da kotu za ta yanke kan shari’ar da ta shafi takararsa.
Read also: Borno: Kwamishinan da ya yi barazanar duka ga ‘yan adawa ya nemi afuwa
“Saboda akwai shari’a a kotu, kotun na iya yanke hukunci dabam. Don haka, amincewar da aka ba shi tana ƙarƙashin duk hukuncin da kotu za ta yanke a ƙarshe,” in ji majiyar.













































