Yanzu-Yanzu: Kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na Kano ya kama mai laifin da ake zargi da tserewa zuwa Fatakwal

FB IMG 1793272853871 750x430

Rundunar haɗin gwiwa ta musamman ta Jihar Kano mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kama Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Keya, mai shekara 27, ɗan asalin Yelwa a Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano, a Fatakwal, Jihar Rivers.

A cewar rundunar, ana zargin Ibrahim da taka muhimmiyar rawa a rikicin faɗan ƙungiyoyin daba da suka addabi wasu sassan Jihar Kano.

Ana zargin Malam Keya da jagorantar wata ƙungiyar daba, tsarawa da ɗaukar nauyin tashin hankalin da ya haɗa da ba wa ’yan daba kuɗi da ƙarfafa su wajen kai hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane, tare da jefa mazauna Ƙaramar Hukumar Dala cikin fargaba.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis ta ce wanda ake zargin ya tsere daga Kano ne bayan rundunar ta ƙara tsaurara ayyukan tsaro a yankunan da rikicin daba ya shafa, ciki har da Jakara, Madigawa, Yalwa, Sanka, Kul Kul, Dogon Nama, Kuka Bulukiya, Dala, Shatsari da Dandalin Turawa.

Sanarwar ta ce jami’an rundunar sun bi diddigin wanda ake zargin zuwa Fatakwal ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka cafke shi a wani samame da shugaban ayyukan rundunar, CSP Bashir Gwadabe, ya jagoranta.

Tun daga lokacin aka dawo da shi Kano.

Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin, shugaban rundunar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, Esq., ya ce “Ina tabbatar muku cewa waɗanda ke ɗaukar nauyin tashin hankali su sani cewa babu nisan da za su je ko wurin ɓuya da zai kare su. Wannan kama farkon abin da za mu yi ne kawai. Ba za mu huta ba har sai an dawo da zaman lafiya gaba ɗaya.”

Kama wanda ake zargin a wajen Jihar Kano na nuna ƙudurin rundunar na bin sawun waɗanda ake nema ruwa a jallo ko da sun tsallaka iyakokin jihar.

A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro, inda za a ci gaba da gudanar da bincike a kansa, sannan a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tanadin doka, tare da tabbatar da cewa ana bin matakan doka da suka dace wajen gudanar da shari’ar duk waɗanda ake zargi.

Rundunar ta tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka, masu ɗaukar nauyinsu da hanyoyin samar musu da miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma, ta yi kira ga al’umma, shugabannin, malaman addini, iyaye da matasa da su haɗa kai wajen yaƙi da wannan matsala ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga ofishin tsaro mafi kusa da su cikin gaggawa, sanya ido kan ’ya’yansu da unguwanninsu, da kuma ƙin yarda kowa ya yi amfani da su wajen kawo cikas ga zaman lafiya.

A ƙarshe, rundunar ta yaba wa rundunonin ’yan sandan Jihar Kano da Jihar Rivers da sauran hukumomin tsaro, bisa goyon baya da jajircewarsu da suka taimaka wajen samun nasarar wannan samame.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here