Dakarun tsaron ƙasar Tunusiya sun ce akalla bakin haure 17 ‘yan kasar Tunisiya da ke cikin kwale-kwalen da ke kan hanyar zuwa Italiya ne suka bace.
Waɗanda ke cikin jirgin da suka haɗa da wani yaro dan shekara biyar sun tashi ne a cikin wani jirgin kamun kifi daga Bizerte da ke arewacin Tunisiya a makon jiya.
Jami’an tsaron teku da na ruwa da ke samun goyon bayan jirage masu saukar ungulu na neman su.
Tunisiya ta karɓe iko daga Libya a matsayin babbar hanyar tashi da bakin haure da ke kokarin shiga Turai daga Afirka.