Wata ƙungiyar Musulunci ta maka NBC da Arewa24 a kotu kan shirye-shiryen da suka saɓa doka

WhatsApp Image 2025 11 01 at 12.41.05 750x314

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Asusun Bincike da Wa’azi na Musulunci da ke Abuja ta shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Kano kan gidan talabijin na Arewa24 da Hukumar Kula da kafafen yaɗa labarai (NBC), bisa zargin karya ƙa’idodin yaɗa shirye-shiryen ƙasa.

Ƙungiyar ta ce ƙarar ta biyo bayan koke-koken da ake yi cewa wasu shirye-shiryen da Arewa24 ke watsawa na ɗauke da abubuwan da ba su dace ba, waɗanda ke cin karo da ɗabi’un al’umma da ƙa’idodin watsa shirye-shiryen ƙasa.

A wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 30 ga Oktoba, 2025, wacce tawagar lauyoyin ƙungiyar A. A. Hikima & Co. suka rubuta zuwa ga hukumar NBC, ƙungiyar ta nemi bayani kan matakan da hukumar ta ɗauka kan shirye-shiryen gidan talabijin ɗin bisa dokar neman bayanai ta shekara ta 2011.

Ƙungiyar ta ambaci shirye-shirye biyu na Arewa24 da suka hada da Mata A Yau da H-Hip Hop, tana zargin cewa suna ɗauke da abubuwan da suka saɓa da tarbiyya da kuma al’adun Arewa, inda ta ce hakan ya jawo suka daga malamai da shugabannin al’umma.

Ta bayyana cewa duk da korafe-korafen da aka shigar kan shirye-shiryen, hukumar NBC ta gaza ɗaukar matakin da ya dace, wanda hakan ya sabawa dokar kafa hukumar.

Asusun ya buƙaci hukumar NBC ta bayyana a cikin kwanaki bakwai bayanan duk rahotanni, bincike, ko hukuncin da ta taɓa yanke kan shirye-shiryen Arewa24, tare da sanar da matsayin amincewa da shirye-shiryen da ake zargi.

Haka kuma, ƙungiyar ta gargadi cewa kin bayar da bayanan cikin lokacin da doka ta tanada zai zama karya dokar neman bayanai, abin da ka iya kaiwa ga ɗaukar matakin kotu don tilasta bin doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here