Wani yaro ƙarami da wasu mutum biyu sun mutu sakamakon wutar lantarki a Kaduna

Kaduna map

Mutane uku, ciki har da yaro ƙarami da yarinya mai shekara 10, sun mutu sakamakon wutar lantarki, yayin da wasu uku suka jikkata a garin Manchok da ke ƙaramar hukumar Kaura a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wata babbar waya ta lantarki ta faɗo kan ƙananan layukan wutar da ke kai wuta gidaje, lamarin da ya haddasa shigar wutar lantarki mai ƙarfi cikin gidaje da muhallin da ke kewaye.

Daya daga cikin waɗanda suka mutu, yaro mai shekara biyu, ya rasa ransa ne bayan ya taɓa cajar waya da aka saka a soket lokacin da aka dawo da wutar lantarki.

Haka kuma, wata yarinya mai shekara 10 ta mutu yayin da take ƙoƙarin gyara zanin da aka shimfiɗa a kan sandar ƙarfe a waje domin busar da shi.

Na uku da ya mutu shi ne Rilwanu Musa, direba, wanda shi ma ya gamu da ajalinsa yayin da yake guga tufafinsa.

Sakataren ƙaramar hukumar Kaura, Haruja Pius, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da buƙatar iyalan waɗanda suka rasu da su karɓi wannan ibtila’i da zuciya ɗaya.

Ya kai ziyara cibiyar kiwon lafiya ta farko da ke Manchok inda ya jajanta wa iyalan, tare da isar da saƙon ta’aziyyar shugaban ƙaramar hukumar, Sankyai Obadiah, kan wannan babban rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here