Twitter zai maka mai Facebook a kotu saboda yi masa kishiya

1d527880 1c8b 11ee 941e 23d1e9ab75fa
1d527880 1c8b 11ee 941e 23d1e9ab75fa

Kamfanin Twitter ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan kamfanin fasaha na Meta game da kirkiro manhajar Threads, don yi masa kishiya.

BBC ta ga wata wasika da lauyan Twitter Alex Spiro ya aikawa shugaban kamfanin Meta da ya mallaki Facebook da Instagram da WhatsApp da kuma Threads Mark Zukerberg, inda a ciki yake zarginsa da satar fasaha da dabarun kasuwanci na Twitter rana tsaka da gan-gan.

Wasikar ta kuma yi ikirarin cewa Meta ya dauki hayar tsoffin ma’aikatan Twitter don taimakawa wajen ƙirƙirar sabuwar manhajar ta Threads.

Barazanar daukar matakin na shari’a da kamfanin na Twitter ya yi a kan kamfanin Meta ba ta zo da mamaki ganin yadda sabuwar manhajar ta kunshi wasu abubuwa na kamanceceniya da Twitter da kuma farin jini da shafin ya shigo da shi.

Kuma bayan haka kamfanin na Meta ya dauki wasu ma’aikata da Twitter ya sallama a lokacin da Elon Musk ya sayi Twitter din aiki.

Bugu da kari daman kamfanin na Twitter ya yi wasu sauye-sauye a tsarinsa wadanda wasu mabiyansa ba su ji dadin hakan ba.

A dangane da hakan wannan sabon shafin na Threads zai kasance tamkar wani zabi ga masu amfani da Twitter da ke da korafi da za su iya karkata gareshi.

Mai kamfanin na Twitter, Elon Musk, ya wallafa wani sako a ranar Alhamis, inda yake cewa: ”Gasa aba ce mai kyau, satar fasaha kuwa ta saba da haka”.

A yanzu dai kamfanin Meta mai wannan sabon shafi, tare da Facebook da Instagram da WhatsApp ya musanta dukkanin zargin da kamfanin Twitter ya yi masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here