Tinubu ya rantsar da Disu a matsayin babban sufeton ƴan sanda na 23

Tinubu and Disu 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin babban Sufeto Janar na ’yan sanda na 23 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A wajen taron, ya kuma rantsar da kwamishinoni shida na Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga, Raba Su da Kula da Harkokin Kuɗi da kuma kwamishinoni biyu na Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Bayan rantsarwar, Disu ya ce jin daɗin jami’ai, dawo da tsaro da kuma shirin kafa ’yan sandan jihohi na daga cikin abubuwan da zai mayar da hankali a kai.

Ya ce an kafa kwamiti domin duba batun ’yan sandan jihohi ta fuskar rundunar ’yan sandan Najeriya, yana mai cewa rundunar ba ta jin tsoron sauyin.

Disu ya amince da cewa rundunar ta dade tana fuskantar ƙalubale kan jin daɗin jami’anta, yana mai cewa aiki na ’yan sanda na da wahala kuma yana da haɗari.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya ya fara ne jim kaɗan bayan kammala rantsarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here