Shugabannin Addini da Al’adu dole ne su fito da hanyoyin dakile cin zarafin mata a kasar nan- Mai Shari’a Fati Abubakar

Justice Fati Abubakar
Justice Fati Abubakar

Uwargidan tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar, Mai shari’a Fati Lamin Abubakar mai ritaya ta kalubalanci shugabannin addini da na al’adu da su jagoranci sabuwar tattaunawa don fito da hanyoyin dakile cin zarafin mata a kasar nan.

Mai shari’a Fati, ta damu matuka kan yadda ake cin zarafi da kyamar jinsin mata a kan wata dabi’a da ta yi daidai da ra’ayin addini da al’adu.

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta bayyana hakan ne a Kano yayin taron tattaunawa ta yini guda da shugabannin addinai da al’adu domin magance yawaitar cin zarafin mata, wanda kungiyar kare hakkin mata ta WRAPA tare da hadin gwiwar cibiyar addinin musulunci ta jami’ar Bayerom suka shirya.

Mai shari’a Fati Lamin Abubakar, wacce ita ce ta kafa kuma shugabar kwamitin amintattu ta WRAPA, ta bukaci masu ruwa da tsaki su yi amfani da rokonsu tare da kara himma wajen samar da “matakan daidaita al’amuran jama’a” don gyatta matsalar.

Yayin da take kokawa kan al’adar yin shiru ga wadanda aka ci zarafin su saboda gudun cin mutuncin al’umma, Mai shari’a Fati ta yi imanin masu ruwa da tsaki za su iya taimakawa wajen dakile matsalar ta hanyar karfafa gwiwar wadanda abin ya shafa su yi magana da kuma samun adalci.

Tsohuwar Daraktar Cibiyar Nazarin Jinsi ta Jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Aisha Ismail, wadda ta jawo alakar zamantakewa da cin zarafin mata da ‘yan mata ta jaddada cewa shugabannin addini da al’adu dole ne su tsara wasu ka’idoji domin sauya tunanin jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here