Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Musa, ya bayyana damuwa kan jinkirin biyan hakkokin fansho na mutanen da suka rasu a cikin ma’aikatan gwamnati.
Ya ce gwamnati na da niyyar tabbatar da gaskiya da saurin biyan waɗannan hakkoki ga iyalan mamatan.
A wata sanarwa da daraktan yaɗa Labarai na ofishin shugaban ma’aikata, Aliyu Yusuf, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa an gudanar da taro tsakanin shugabannin hukumomi masu ruwa da tsaki domin duba matsalar.
Taron ya samu halartar shugaban hukumar kula da asusun Fansho ta Jihar Kano, babban sakatare na Kotun Shari’ar Musulunci mai wakiltar Babban Alkalin Shari’a, da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.
A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan matsalolin da ke haifar da jinkirin biyan hakkokin, kuma sun cimma matsaya kan wasu muhimman matakai da za su taimaka wajen magance lamarin.
Yayin taron an gano cewa hukumar kula da asusun fansho na gudanar da aikinta yadda ya kamata ta hanyar tura kuɗi zuwa kotunan shari’a domin rarraba su ga masu hakki bisa umarnin kotu.
Bayan doguwar tattaunawa, taron ya amince cewa tsarin biyan kuɗi ta hanyar kwamfuta da kotunan suka fara amfani da shi don tabbatar da gaskiya da kauce wa rashin daidaito, ya ci gaba da aiki.
Haka kuma, an yanke shawarar cewa hukumar kula da asusun fansho za ta ci gaba da tantance bayanan mamata da tabbatar da sahihancin jerin iyalan da za su karɓi kuɗi kafin a mika wa kotunan don biyan su.
Taron ya kafa kwamitin mutum uku da suka haɗa da shugaban ma’aikata a matsayin shugaban kwamitin, babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci, da shugaban hukumar asusun Fansho ta Jihar Kano.
Aikin kwamitin shi ne gano matsalolin da ke haifar da tsaiko da kuma samar da hanyoyin da za su hanzarta biyan hakkokin.
Kwamitin zai kuma tattauna da alkalan kotunan shari’a da ma’aikatan kudi domin duba yadda za a gudanar da biyan kuɗin cikin sauƙi da tsari.
An tsara cewa za a sake gudanar da wani taro a ofishin Shugaban Ma’aikata domin nazarin rahoton binciken kwamitin da kuma ɗaukar matakan da suka dace.













































