Wani mummunan lamari ya faru a unguwar Makwarari da ke jihar Kano, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kai ga rugujewar wani gida wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wata uwa mai suna Balaraba Tijjani mai shekaru 35 da raunata ‘ya’yanta guda biyu a ranar Juma’a.
SolaceBase ta rahoto cewa yaran Abdulnasir ne da Abdallah, masu shekaru 11 da 13.
A cewar mijin, Tijjani Magaji, ruwan sama mai karfi da ya fara a daren ranar Alhamis ya kuma ci gaba da zuwa da safiyar Juma’a ne ya sa ginin ya ruguje.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ginin gidan zama ne na wani bene.
“Mun samu kiran gaggawa a ranar Juma’a, da misalin karfe 9:30 na safe, daga dakin kula da lafiyarmu daga wani ma’aikacin mu Ibrahim Isah, cewa wani gini ya ruguje.
“Bayan samun labarin, mun aika da ‘yan kwana-kwana cikin gaggawa zuwa wurin,” in ji shi.
Abdullahi ya bayyana cewa an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a raye kuma an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin yi musu magani.