Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa birnin Nairobi domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Kenya, William ruto.
Taron da zai gudanar a talatar nan a filin wasa na Kasarani dake Nairobi, shine karo na biyar na rantsar da shugaban kasa a Kenya.
Osinbajo wanda ya samu tarba a filin sauka da tashin jiragen sama na Jomo Kenyatta da ke Nairobi daga tsohon gwamnan yankin Kwale, Salim Mvurya da jakadan Najeriya a Kenya Yusuf Yumusa da sauran manyan jami’an gwamnati.
A ranar 15 ga watan Agusta ne hukumar Zaben Kenya ta ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Agusta.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Wafula Chebukati, ya ce Ruto ya lashe kusan kuri’u miliyan 7 da doriya kwatankwacin kashi 50.49 cikin 100, yayin da abokin hamayyarsa Raila Odinga ya samu kuri’u miliyan 6.94 ko kuma kashi 48.85.
Kotun kolin Kenya, a ranar 5 ga watan Satumba, ta tabbatar da nasarar da Rutho ya samu a zaben.
Mataimakin shugaban kasar yayin bulaguron yana tare da karamin ministan harkokin wajen Najeriya Amb. Zubairu Dada, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Sen. Babafemi Ojudu.
Najeriya da Kenya, wadanda kasashe ne rainon ingila tayiwa mulkin mallaka, suna da kyakkyawar alaka ta diflomasiyya kuma sun kulla yarjejeniyoyin kasuwanci da noma da dai sauransu dan cigaban junan su.
(NAN)













































