Wani dan siyasa a nan Kano, Nasiru Koguna, ya yi ikirarin cewa har yanzu shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, a Kano, ba Sha’aban Sharada ba.
A wata wasika da ya aike wa hukumar zabe ta kasa INEC, Nasiru Koguna, ta hannun lauyansa Farfesa Nasiru Aliyu, Mai mukamin SAN, ya ce wakilan jam’iyyar sun zabe shi bisa ka’ida a matsayin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar.
Ya kara da cewa shi da kansa bai rubuta wa hukumar zabe ta INEC sanarwar janyewa ba kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.
“Ina aiki a matsayin Lauya ga HON. NASIRU HASSAN KOGUNA mamba ne dake da katin jam’iyyar ADP, kuma a madadinsa da umarninsa muka rubuta wannan wasika,” kamar yadda wasikar ta bayyana.
“Za ku iya tuna wanda nake karewa shi ne dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADP a babban zaben 2023 mai zuwa.
Sakamakon haka jam’iyyar ta tura sunan Wanda muke karewa ga hukumar ku. Cewa jam’iyyar ta amince ta maido wa wanda muke karewa duk wasu makudan kudade da ya kashe wajen tsayawa takara da yakin neman zaben da ya yi.
Jam’iyyar ta yi alkawarin tsayar da wanda muke karewa a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben gwamnan jihar Kano.
Matukar ya janye takararsa shi ne zai cike takardar INEC ta sanarwar janye takararsa da kansa sannan kuma ya mikata da kansa ga hedikwatar Jam’iyyar ADP ta kasa da ke Abuja.
“Wanda muke karewa ya bayyana mana cewa domin ya nuna muhimmancinsa da jajircewarsa ga Shugaban Jam’iyyar na kasa, ya aika da sanarwar karyata ficewa daga jam’iyyar ta manhajar WhatsApp, yana jiran jam’iyyar ta yi abin da ya dace.













































