Naira dubu 70 bata wadata: Ƙungiyar ƙwadagoNLC da ma’aikata sun nemi a sake duba mafi ƙarancin Albashi

NLC

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnatin tarayya sun bukaci a sake duba mafi ƙarancin albashi na ƙasa, suna mai cewa naira 70,000 da ake biya yanzu ya gagari rayuwa.

A wata tattaunawa daban daban da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya yi da ma’aikatan, sun bayyana cewa hauhawar farashin kaya, abinci, sufuri, gidaje da sauran muhimman bukatu sun sa wannan albashi baya isa.

A watan Yuli 2024 ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da ta ɗaga mafi ƙarancin albashi daga naira 30,000 zuwa 70,000, sai dai daga baya jihohi da dama sun ƙara sama da haka, inda Imo ta ɗaga zuwa N104,000, Lagos da Rivers suka sa N85,000, yayin da wasu kamar Bayelsa, Enugu, Akwa Ibom da Niger suka ɗora N80,000, sannan wasu kamar Delta da Ogun suka biya Naira 77,000.

Sakataren NLC, Benson Upah, ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya lalata ƙimar naira 70,000, don haka gwamnati na da alhakin ɗaga shi cikin gaggawa, inda ya yi gargadin cewa idan tattaunawa ta gaza, akwai yiwuwar ƙwadago ya ɗauki matakin yajin aiki.

Karanta: NLC ta yi barazanar mamaye ƙasar nan da Zanga-zanga sakamakon karin farashin wutar lantarki

Shugaban ƙungiyar manyan ma’aikata (ASCSN), Shehu Mohammed, ya yaba wa gwamnonin da suka ɗaga albashi, yana mai cewa tuntuni ƙungiyoyin ƙwadago sun nemi albashin da ya kai naira 250,000 , yana mai cewa biyan 70,000 ba ya wuce ɗaukar ma’aikaci daga gida zuwa wurin aiki kawai.

Wasu ma’aikatan gwamnati da aka zanta da su sun bayyana ƙalubale iri-iri da suke fuskanta, musamman wajen biyan haya, kudin makaranta, da kuɗin abinci. Wasu sun ce kudin ya kare kafin ƙarshen wata, wasu kuma sun nuna cewa wannan matsin lamba yana jefa iyalai cikin ƙunci da talauci.

A cewar wasu, ɗaga albashi ba wai kawai don gamsar da ƙwadago ba ne, illa dai don dawo da mutunci da ƙima ga aiki da kuma tabbatar da adalci tsakanin gwamnati da jama’a. Sun yi kira da a ɗaga mafi ƙarancin albashi zuwa akalla naira 150,000 tare da samar da manufofin rage tsadar rayuwa kamar gidaje masu sauƙi, sufuri da kiwon lafiya.

Haka kuma, sun jaddada cewa idan ma’aikata sun samu isasshen albashi, za su kasance masu ƙwazo, kishin aiki da kuma nisantar cin hanci, wanda hakan zai inganta ayyukan gwamnati da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here