Masu neman aiki su 8 sun fadi a gwajin ƙwaya da TESCOM ta yi musu

abdulrahman abdulrazaq (1)

Hukumar kula da aikin koyarwa ta jihar Kwara (TESCOM) ta ce takwas daga cikin mutane 1,800 da aka zaba domin aikin koyarwa sun faɗi sakamakon yadda gwajin su ya nuna suna tu’ammali da haramtattun kwayoyi.

Wata sanarwa daga sakataren yada labarai na TESCOM, Sam Onile ya fitar a ranar Litinin a Ilorin, ta ce kai tsaye sun yi asarar kujerunsu a wannan lokaci na daukan ma’aikata.

Karin karatu: Ka cika alkawarin da ka ɗauka a lokacin yakin neman zabe na hada tarukan tattaunawa – Kungiya ta bukaci gwamna Ododo

A cewar Onile, Shugaban Hukumar TESCOM, Bello Taoheed, ya ce masu neman aikin sun yi gwajin magungunan da suka hada da benzodiazepine, tramadol, cotinine, marijuana da amphetamine – wadanda ake ganin ba su da hadari ga lafiyar dan Adam.

Ya ce hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ce ta gudanar da gwajin tare da cikakken goyon bayan Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here