Mashaƙo ta kashe yara bakwai, ta kwantar da 22 a asibiti a Yobe

1689165362122
1689165362122

Cutar mashaƙo ta kashe yara akalla bakwai bayan ɓarkewarta a karamar hukumar Potiskum na jihar Yobe.

Hakazalika ta kuma kwantar mutum 22 a asibiti.

Yankunan da aka bayyana ɓarkewar cutar sun haɗa da Tandari da Titin Misau da Sabuwar Sakateriya da Arikimr da Ramin Kasa da Boriya da Igwanda da kuma rukunin gidaje na Texaco.

Wani mutum a asibitin kwararru da ke Potiskum, ya faɗa wa gidan talabijin na Channels cewa asibitin ba shi da isasshen magani da zai iya shawo kan cutar ko kuma kula sa marasa lafiya.

Ya kuma bayyana cewa cikin yara 22 da aka kai asibitin a ranar Litinin, biyu daga ciki sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.

Sai dai jami’an lafiya a jihar ba su kai ga tabbatar da mutuwar yaran ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here