Lauyoyi, kamfanoni, dole ne su biya kashi 7.5% na harajin VAT a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji – Gwamnatin Tarayya

New Tax Reform 640x430

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa dukkan lauyoyi da kamfanoninsu ya zama wajibi su biya kashi 7.5 cikin ɗari na harajin kayayyaki (VAT) ga hukumar tara haraji ta cikin gida (FIRS), bisa sabon tsarin haraji da za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Gwamnatin ta bayyana cewa ayyukan lauyoyi na cikin rukunin ayyukan ƙwararru da ke ƙarƙashin haraji bisa sabon tsarin kuɗi.

Sai dai ta fayyace cewa ’yan kasuwa, jami’an soja, ma’aikata da ke samun ƙasa da naira dubu 800 a shekara, da ƙananan ’yan kasuwa masu juya kuɗi ƙasa da naira miliyan 100, ba sa cikin waɗanda dokar ta shafa.

Dokar ta bayyana cewa idan aka caje VAT ga wanda bai kamata ba, za a iya mayar da kuɗin cikin kwanaki 30.

Shugaban hukumar FIRS, Dakta Zack Adedeji, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron shekara na 56 na ƙungiyar malamai masu koyar da aikin lauya ta Najeriya (NALT) da aka gudanar a jami’ar Abuja.

Ya bayyana cewa manufar wannan sauyin haraji ba wai don ƙara wa ƙwararru nauyi ba ce, sai don tabbatar da adalci da gaskiya a tsarin tara kuɗaɗen shiga na ƙasa.

Ya ƙara da cewa tsarin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati wajen faɗaɗa fagen tara haraji, hana kauce wa biyan haraji, da ƙarfafa kuɗaɗen shiga domin ci gaban ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa doka ta bai wa hukumar FIRS ikon naɗa wasu wajen tattara harajin daga waɗanda ke waje da ƙasar, tare da jan hankalin lauyoyi da su yi rijista da FIRS, su rika gabatar da bayanan haraji, da biyan VAT akan lokaci, inda ya gargadi masu ƙin bin doka da hukunci.

A nasa jawabin, Farfesa Abiola Sanni, babban lauya kuma shugaban sashen koyar da doka na jami’ar Legas, ya bayyana sabbin dokokin haraji guda huɗu a matsayin ci gaban tarihi a harkar tattalin arzikin Najeriya, tare da kira ga gwamnatocin jihohi su daidaita tsarin harajinsu da na tarayya domin tabbatar da zaman lafiyar kuɗi da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa, jihohi su taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun haraji da tabbatar da gaskiya a amfani da kuɗaɗen gwamnati, musamman a fannoni kamar gine-gine, ilimi da kiwon lafiya, tare da ƙarfafa wayar da kai ga jama’a don sauƙaƙa aiwatar da dokokin harajin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here