Kwamitin Shura na Shekarau ya ki amincewa da sauya shekarsa daga NNPP zuwa PDP

Ibrahim Shekarau new
Ibrahim Shekarau new

Babban zauren tuntuba da ke yanke hukunci kan tsarin tafiyar mabiya imanin siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, wato Shura Consultative Assembly, ta yi watsi da yunkurin da jam’iyyar PDP ta yi na ganin tsohon gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

A wani taro da aka yi a ranar Lahadi 14 ga watan Agustan Shekarar da muke ciki ta 2022 a gidan Malam Shekarau, dake Mundubawa, a Kano, wanda ya dauki tsawon sa’o’i biyar ana tattaunawa akan batun da sauran abubuwan da aka yi watsi da su, ciki har da batun ficewa daga jam’iyyar NNPP bisa zargin cewa Dan takarar Shugabannin Kasa na Jam’iyyar Sanata Rabiu Kwankwaso bai cika yarjejeniyar da suka kulla da Malam Ibrahim Shekarau ba kafin ya koma jam’iyyar ta NNPP a baya-bayan, kamar yadda wata majiya mai karfi ta tabbatar wa Jaridar Solacebase a ranar Talata.

“Ka san Malam Shekarau ya dauki matakin sauya sheka ba tare da tuntubar majalisar Shura ba,” inji majiyar take bayyana wa Jaridar Solacebase.

Wata jarida ta kafar Internet,Mai suna Daily Nigerian ta ruwaito shirin sauya shekar Malam Shekarau zuwa jam’iyyar PDP.

A cewar jaridar, majiya mai tushe da ke da masaniya kan yunkurin Malam Shekarau da kuma ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da Shugaban jam’iyyar na kasa Iyochia Ayu, ya ce tsohon gwamnan ya “yi yarjejeniya” da PDP kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

Jaridar ta tattaro cewa wani kwamiti mai mambobi 21 zai gana a ranar Talata 16 ga watan nan da muke ciki na Agusta da misalin karfe 4 na yamma don kammala shirye-shiryen sauya shekar.


Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta ce a wani bangare na shirin ficewar, dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar zai je gidan Malam Shekarau dake Mundubawa a Kano domin ya yi masa rakiya kafin a fitar da sanarwar.

“Gaskiyar magana ita ce Atiku ya yi wa Mallam wasu ta yin romon baka kamar na samar da guraben ayyuka a Hukumomi da ma’aikatun gwamnati, baya ga nada shi a matsayin kodinetan yakin neman zaben yankin Arewa maso Yamma da kuma kula da kudaden yakin neman zabe a yankin,” in ji majiyar ga jaridar Solacebase.

Sai dai da yake tabbatar da tattaunawar da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, wani na kusa da Malam Ibrahim Shekarau ya shaida wa Jaridar Solacebase cewa babbar jam’iyyar adawa da sauran wasu Jam’iyyun sun tattauna da Malam Shekarau kan ya fice daga jam’iyyar NNPP.

”Ka ga dole ne na fayyace maka gaskiya cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a matakin kasa suna zawarcin Malam ya watsar da jam’iyyar NNPP koma PDP duba da irin halayensa da kuma dimbin mabiyan da yake da su ta yadda Wazirin Adamawa zai lashe zaben 2023,” inji majiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here